8 Nuwamba 2021 - 12:15
Abdollahian : An Yi Yunkurin Kashe Al-Kazemi Ne Da Nufin Tada Zaune Tsaye A Iraki

Ministan harkokin wajen Iran, ya bayyana yunkurin kashe firaministan Iraki, a matsayin wani al’amari na neman tada zaune tsaye a kasar ta Iraki.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Irakin, ministan harkokin wajen kasar ta Hossein Amir-Abdollahian, Iran ya yi tir da yunkurin kisan gillar da aka yi wa Firaministan Iraki.

Fira Ministan Iraki Mustafa al-Kazemi ya tsallake rijiya da baya ne bayan wani yunkurin hallaka shi da wani jirgi mara matuki dauke da ababen fashewa.

Hossein Amir-Abdollahian ya shaidawa ministan harkokin wajen Iraki Fouad Hussain cewa irin wadannan abubuwa sun sabawa tsaro da zaman lafiyar kasar ta Iraki.

342/